Dating| Hook Up | Leak Photos | Sugar Mummy |Sugar Daddy | Health Tips | Celebrity News | Love Story

Search Our Blog Below

Ana zanga-zanga a jihar Ekiti saboda Fayose

– Wasu gamayyar kungiyoyi sunyi zanga-zangar nuna kin jinin Fayose a Ado Ekiti jiya

– Sun bayya acewa gwamnan baya son tafiyar da gwamnati cikin adalci

– Sun zargi yan majalisa da yin karya a game da kamasu da suka ce jami’an DSS sukayi

– Sun bayyana cewa yan majalisar da ake nema suna cikin gidan Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

Wasu gamayyaun kungiyoyi sunyi zanga-zanga a jiya a Ado Ekiti inda suka zargi gwamnan Fayose da kin tafiyar da adalar gwamnati a jihar.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya tattauna da masu neman Biafra – Anohu

Jaridar The nation ta ruwaito cewa kungiyoyin sun bayyana aiyukan gwamna Fayose a matsayin masu kawo wahala ga jama’a. Sannan kuma sun musanta cewa jami’an DSS sun shiga majalisar jihar domin su kama wasu yan majalisa.

Gamayyar kungiyoyin kuma sun bayyana goyon bayan su ga yaki da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi inda suka bayyana cewa duk wanda ya saci kudin Najeriya dole ya maida dasu.

Sannan kuma sunyi kira a binciki gwamna Fayose akan rashawar data faru lokacin

zaben jihar, da kuma akan kaddarorin da yake dasu a Abuja, Afirika ta kudi, Ghana da kuma Dubai.

Masu zangar-zangar sun rike takardu wadanda aka rubuta:

” Masu goyon bayan juyin mulki dole a hukunta su. Yauushe Fayose zaya bayyana kaddarorin shi? Babu wani abu kamar DSS  sun shiga majalisa. Ka daina rushe kasuwanni. Ka bar amfani da matasan Ekiti a matsayin yan daba.

Kimanin kungiyoyi 4 ne sukayi zanga-zangar. Sun fara n da mkisalin karfe 9 na safe na jiya. Bayan da suka gama, Adedamola Temitayo ya bayyana cewa ya kamata a binciki Faypse saboda Naira Biliyan 2.4 na gyara muhalli ta bacce tun hawan shi gwamna.

A wani labarin kuma, gwamna Fayose yayi Allah wadai da tafiyar da Buhari yake yi kasashen waje. Yayi kira ga shugaban kasa ya zauna Najeriya.

Source : Link N

Source : Link KL

Share:

Related Posts:

No comments:

Post a Comment

Popular Posts

Labels

Blog Archive