– Yinusa ya bayyana cewa shi yayi ma Ese Oruru ciki
– An gurfanar dashi gaban Kotu
Yinusa a kotun Bayelsa
YInusa Dahiru, wanda ake zargi da sace wata yarinya yar shekara 14 mai suna, Ese Oruru, daga jihar Bayelsa zuwa jihar Kano inda ya aure ta, ya gurfana gaban babbar kotun tarayya dake a Bayelsa inda ake tugumar shi da lalata da karamar yarinya, saduwa da mace da kuma sace mutum.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Yinusa ya amsa ma kotu cewa shi yayi ma Ese ciki, amma daga bakin Yan Sanda ya fara jin cewa cikin watan shi 5.
Ku karanta: Ese Oruru ta koma Bayelsa
Mahaifiyar Ese Oruru tayi Allah wadai da yadda aka baza labarin inda ta bayyana cewa iyalan su Yinusa da nasu ba bakin bane domin sun saba da juna da dadewa kafin aukuwar wannan lamarin.
Source : Link N
No comments:
Post a Comment